An Kama Dan Sanda Mai Yiwa ‘Yan Achaba Kwacen Baburansu A Bauchi

A kokarin rundunar Yan sanda ta jihar Bauchi na share hawayen jamaa musamman Yan acaba, game da kwace mashinan jamaa da ake zargin wasu bata garin yan sanda na Yi, rundunar ta sallami wani sajen yan sanda daga aiki ranar litinin 22/6/2020.

Kwamishinan Yan sandan jihar Bauchi Alhaji Lawan Tanko jimeta, a lokacin da ya kama aiki a kwanakin baya ya ci Karo da korafin mutane na zargin wasu yan sanda na karbe mashinan mutane suna kaiwa gidajensu idan an wana biyu su sayar ko su canja musu fasali suna hawa.
Lawan Tanko jimeta yayi alkawarin bincika irin wadannan yan sanda tare da hukunta su a matsayin barayi masu zamba cikin aminci.
Don haka rundunar Yan sandan ta sallami Sajan Makama Musa dan shekara 34 dan asalin jihar Gombe, saboda an same shi cikin kayan sarki na yan sanda ya karbe mashin kirar boxer mai lamba DBM-319-UR Bauchi.

Rundunar ta ce mutanen yankin yalwa da hanyar Dass sun jima suna zargin Dan sandan wajen kwace mashinan jamaa da sunan kama Yan acaba.
Rundunar ta bayyana cewa tuni an mika shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar SCID don gurfanar da shi a gaban kotu.

Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar Ahmed Mohammed Wakil, ta ja hankalin jama’a su taimaka musu don bayyana asirin bata gari a magance su.
Tun daga lokacin da aka fitar da doka kan hawa mashin a jihar Bauchi an samu korafin wasu bata garin Yan sanda suna kwace mashinan jamaa suna sayarwa ko suna mallakawa kan su, yadda mutane a unguwar Gudum suka bayyana cewa anga mashin hudu a gidan wani Dan sanda. Saboda haka ne rundunar ta himmatu wajen magance wannan matsala kuma ta nemi jama’a su bata goyon baya da bayanai na gaskiya da hujjoji na zahiri don gudanar da aikin ta kan wannan matsala.

Daga Muazu Hardawa a Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *