An Kama Almajiri Dan Shekaru 10 Yana Yunkurin Lalata Da Akuya

Duk da cewar labari ne marar dadin ji Amma zan daure na bayar, wasu mutane a wata unguwa a Kano suna daga cikin gidan su ka hango wani kankanin almajiri da Bai wuce Shekara 10 ba yana yunkurin yin lalata da Akuya, nan da nan mutanen suka kama shi daga baya suka tuhume shi yake shaida musu cewar wani gardi ne yake koya musu abin babu dadin ji.

Yanzun Haka in takaice muku labarin an kai Kara gun yan civil depence kuma sunzo sun kama wanda ake zargi shine ya koyawa Yaron, Har ma an gano wasu yaran wadanda Suma duk ya lalata su.

Yanzun fargabar al’ummar wannan unguwa shine basu San adadin yaran da aka koyawa wannan muguwar ta’ada ba, sannan basu San adadin wadanda sukuma yaran suka koyawa ba, Dan Haka, suke cikin tsaka Mai wuya, duk da cewar am zo an kama wannan mutum Amma fa akwai sauran rina a kaba, domin Har an fara bibiyar wasu daga masu ruwa da tsaki Akan shigar da karar cewar wai a dawo da maganar gaban kwamitin unguwa, Har na wasu fara cewar wai kaddara ce tana iya afkawa kowa.

Yanzun Dai shi wannan mutum yana hannun yan sibil defens, har kuma wata majiya tace binciken su yayi Nisa.

To Bari su za a yi su kammala binciken ko kuwa za a dawo da maganar gaban kwamitin unguwar? Ni dai zan fison ace abar hukuma tayi bincike ta hukunta duk me laifi, Amma Dai shan koko daukar rai.

Allah Dai ya shiga tsakanin nagari da mugu…

Daga Shafin Nasiru Salisu Zango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *