An Daga Ranar Binne Tsohon Gwamnan Oyo Ajimobi

An ɗage ranar da za a yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, sutura.

Mai magana da yawun Marigayin Bolaji Tunji ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma’a.

“Iyalan marigayin za su sanar da lokacin da za a yi masa jana’iza nan gaba kadan.

“Jana’izar za ta kasance a kebance saboda biyayya ga dokokin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC)”, inji Mista Tunji.

Ya kuma yi kira ga mutanen da ke tururuwa zuwa gidan marigayin domin ta’aziyya da su bi matakan kariya daga kamuwa da COVID-19 kamar yadda hukumar NCDC ta zayyana, ciki har da wanke hannaye, da sanya takunkumin rufe fuska da kuma ba da tazara.

Marigayi Abiola Ajimobi ya rasu ne ranar Alhamis a wani asibiti mai zaman kansa a Legas bayan ya yi fama da wata jinya mai alaka da sarkakiyar da cutar coronavirus ta haddasa.

Yanzu haka dai a faɗin tarayyar Najeriya,  ana ci gaba da mika sakon jaje da ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *