2023: Mun Amince Da Tattaunawa Kan Fidda Ɗan Takara – Matasan Arewa


Gamayyar kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya sun bayyana cewar sun samu fahimtar juna da takwarorinsu dake yankin Kudancin kasar domin fitar da ɗan takarar da ya dace wanda zai jagoranci ƙasar wajen kaita tudun mun tsira daga Iftila’in da ya fada mata.

Shugaban Matasan Arewan Alhaji Yerima Shettima ya bayyana hakan lokacin tattaunawar shi da manema labarai a Kaduna dangane da batun shekarar zabe ta 2023 dake tunkarowa.

Matasan na Arewa sun ƙara da cewar tuni zama ya yi nisa a tsakanin su da matasan Kudu musamman na ƙabilar Inyamurai wato Ohanaeze inda za suyi aiki tare ba tare da bambancin addini ko kabila ba wajen ceto Najeriya.

Shettima ya cigaba da cewar su a matsayin su na matasa babu wata jam’iyya da suke da alaƙa da ita walau PDP ko APC, sai dai kawai abin da suka sanya gaba shine yadda zasu ceto kasar daga wargajewa.

Akwai shirin da muke da shi na samar da wata jam’iyya ta matasa domin fuskantar ƙalubalen da ƙasar ke ciki. Lokaci ya yi da zamu haɗa kawunanmu domin samawa jama’a musamman matasa mafita a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *