Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Tare Da Sace Shanun Al’umma A Jahar Neja

Labarin da muke samu na bayyana cewar a daren jiya gungun wasu barayi ɗauke da muggan makamai sun kai hari a ƙauyen Tashan Mahaukaci dake ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja inda suka kashe wani mutum guda tare da raunata mazauna ƙauyen dadama su ka kuma kwashe dabbobin su wanda sun kwashi shanu kimanin ɗari biyar kamar yadda wani mazauni yanki ya tabbatar mana.

Yanzu haka al’ummar ƙauyen na cigaba da yin hijira suna barin yankin domin fargabar abunda ka iya biyo baya, sun kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wurin yaƙi da ta’addanci da takeyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *