Ƙarya Yahaya Bello Ya Kai Game Da Komawar Gwamnonin Jam’iyyar Zuwa APC – PDP

Jam’iyyar PDP tace wannan bayanan da Yahaya Bello yayi shirmene kawai da shiririta, inda yace wasu daga cikin gwamnonin PDP suna kokarin komawa jam’iyyar da batasan inda gaban ta ya dosa ba ta APC a matsayin abun dariya , shirme da shiririta.

Jam’iyyar tace irin wannan zancen na shiririta shine yasa babu wanda a Najeriya yake ganin Gwamna Bello da muhimmanci.

PDP tace wannan bayanan na gwamna Bello bakomai bane sai kokarin dauke tunanin mutane daga kan dambarwar da take faruwa a APC .

Yan Najeriya suna sane da cewa Bello bashi da alaka da gwamnoni uku a APC .Babu wani gwamna a APC da yake sha’awar hada alaka da Bello a bayyane, dadin dadawa, baza ka samu Gwamna uku da suke ganin mutuncin sa ba.

Hakika Bello bashi da alaka da wani Gwamna da yake jam’iyyar PDP , wannan halinsane, ya shiga gidan talabijin, yana fadar karya .

Abin da kowa ya sani babu wani wanda zai dau wannan karyar a ce mutumin da yake PDP , zai koma rusasshiyar APC .

Wannan ya nuna cewa babu hadin kai a APC, wanda suka kwana suna tattaunawa saboda kullum mutanen su suna komawa PDP , kuma jagororinsu ma suna kan hanya tunda APC ta mutu kurmus.

Abun kunyar , shi Gwamna Yahaya Bello yasan babu wata jam’iyya da zata karbesa, babu wata jam’iyyar da zata karbesa bayan rushewar APC, shiyasa ya kidime da fadar karya domin ya nuna APC tana nan.

Okey Sa hannu
Kola Ologbondiyan
Sakataren watsa labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *