Yadda Dan Damfarar Najeriya Hushpuppi Ya Damfari Mutane Miliyan 2 Kudaden Da Adadinsu Ya Kai Dala Miliyan $435.6

‘Yan sandan Dubai sun bayyana cewa, fitaccen dan Nijeriyan nan da ya yi shuhura akan kafar yada zumunta ta Instagram, wato Raymond Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, ya damfari mutane miliyan daya da dubu dari tara da ashirin da shida da dari hudu (1,926,400).

‘Yan sandan Dubai sun cafke Hushpuppi ne a ranar 10 ga wannan wata na Yuni, inda a jiya Alhamis, hukumomi a Dubai din suka ssaki wani gajeren bidiyo da ke nuna jimillar ayyukan damfara da Hushpuppi ya aikata a jimlace.

Hushpuppi da dabarsa da ke aikata zamba a fagen yanar gizo sun damfari mutane sama da miliyan 1.9 kudade a dalar Amurka da yawansu ya kai miliyan $435.6

An same su da laifin aikewa mutane da sakon email na bogi, da kuma karkatar da kudaden da aka turo ta yanar gizo zuwa asusun ajiyarsu.

Bayan tsawon watanni suna bincike, yan sandan Dubai sun yi nasarar bankado wannan daba ta su Hushpuppi, inda suka kai musu hari suka kama su a lokacin suna bacci a dakunansu a Dubai.

Hushpuppi na yawan nuna alfahari da irin dukiyar da ya ke da ita ta hanyar wallafa hotunansa da ke nuna rayuwa mai tsada da ya ke yi.

Hushpuppi ya taba bayyana cewa shi din dan kasuwa ne wanda ya yi nasarar a harkar kasuwancin da ya ke gudanarwa

Kafin cafke dabar ta su Hushpuppi, akalla sun damfari mutane na adadin Dirhamin Dubai biliyan data da miliyan 600.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *