Uwargidan Gwamna Jahar Bauchu Ta Tallafawa Mata Domin Dogaro Da Kai

Gidauniyar Al-Muhibba assasawar Uwargidan Gwamnan Bauchi, Hajiya Dakta Aishatu Bala Mohammed ta baiwa mata guda 250 tallafin dogaro da kai a kauyen Gwana dake karamar hukumar Futuk a jihar Bauchi.

A yayin rabon rabon tallafin, Uwargidan Gwamnan ta yi kira ga matan da suka amfana da tallafin da su mayar da hankali wajen gudanar da sana’o’insu don ganin su ma sun tsaya da kafsfun su don ganin su ma sun taimakawa wasu a nan gaba.

Hamsin daga cikin matan kowacce ta samu tallafin jakar ledar ruwa (pure water) guda ashirin, yayin da wasu hamsin din suka samu tallafin injin sarrafa taliya ‘yar murji. Sai kuma guda 150 kowaccen daga cikin su ta samu tallafin naira dubu biyar.

Haka kuma Uwargidan Gwamna ta kafa cibiyar yaki da jahilci mai taken ‘tsufa ba ya hana neman ilmi”, inda za a dinga karantar da ilmin addini da na zamani.

An kaddamar da cibiyar ne a karamar hukumar Alkaleri tare da niyyar fadada shirin a duk fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *