Sha’awa, Babban Tarkon Shai’dan – Daga Zauren Fiqhu

SHAI’DAN IBLEES (L. A) yana da kofofi da yawa wadanda yake biyowa ta cikinsu domin hallakar da ‘Dan Adam.. Kuma yana da wasu miyagun tarkona masu cike da guba wadanda yake ‘dandana ma ‘dan Adam domin kamashi.

Idan Shai’dan ya bullo maka ta hanyar Shirka yaga ka tsallake, sai ya bullo maka ta hanyar bidi’a.. idan yaga ka tsallake, sai ya fara zuga ka.. ya bullo maka ta hanyar RIYA… Ya san zai yi wuya ka tsallaketa..

Idan ya bullo maka ta hanyar CIN AMANA, yaga ka tsallake, sai ya bullo maka ta hanyar tsananin son duniya da kuma dogon buri.. – Zai yi wuya ka tsallake.

Idan ya bullo maka ta hanyar Kasala yaga bai ci nasara ba, sai ya bullo maka ta hanyar girman kai da Taqama… da jin cewa kai wani ne… – Zai yi wuya ka tsallake.

Idan duk bai zo maka ta wannan wajen ba.. ko kuma yazo amma bai samu nasara ba, sai ya bullo maka ta hanyar SHA’AWA.. yace maka ai kai matashi ne.. kana da karfin sha’awa. Mai zai hana ka rika aikata wani abu din rage Qarfin sha’awarka?

Idan kuma ke budurwa ce ko matar aure, sai ya nuna miki cewa yanzu yadda kike da kyawun diri da kyawun fuska, mai zai hana ki rika yin kaza-da-kaza domin jan hankalin samari da sauran Mazajen da suke waje??

Idan kuma kika dubi fuskarki a mudubi sai ya sake zugaki… Yanzu yadda kike din nan……

Daga nan sai ya fara chusa ma mutum tsananin sha’awa, yana Qara ingizaka cikin abubuwan da zasu sanya sha’awarka ta kara tsananta.. kamar kallon fina finai na batsa, shafukan internet na batsa, Zantukan batsa tare da Qawaye ko abokai, Chudanya da ‘daya jinsin, etc.

Ramin sha’awa yana da zurfi kwarai da gaske. Idan ka afka cikin Zina da Luwadi ko Madigo ko Istimna’i, to hakika shaitan yaci riba akanka..

Ya riga ya kamaka/ya kamaki acikin tarko mafi hatsari… Tarkon da yake lalata Rayuwar mutum ta duniya, ya Quntata masa rayuwar Qabarinsa, sannan ya Jefashi cikin nadama da azaba mafi tsanani awutar Jahannama..
‘Yan uwa mu yawaita tuba zuwa ga Allah, mu nemi tsari daga babban makiyinmu (Shai’dan) mu kiyayi bin son zuciya..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *