N-Power Ta Fitar Da Sabon Jawabi Ga Masu Neman Shiga Tsarin


N-Power wacce ta kasance shirin gwamnatin tarayya na Tallafawa matasa Masu takardar kammala makaranta marasa Aikin yi a ranar ta bada sabon jawabi game da shirin daukar sabbin ma’aikatar 2020 da za ta yi inda ta bayyanawa Matasa yadda za su shirya cike fom din a yanar gizo.

N-Power ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter .

Sun ce: “ Ya ku masu niyyar cika fom din shirin N-Power 2020,

“Ga yadda za ku shirya cika fom din N-Power

“Ku tuna,”

”1. Za a bude shafin cika fom din da misalin karfe 11:45 na daren 26 ga watan Yuni, 2020.


“2. Cika fom din a yanar gizo kyauta ne ba sai an biya kudi ba. KA DA ku biya kowa kudi wajen cika fom din N-Power a yanar gizo.


“3. Ku sami takaitacccen Takardar BVN na ku.

Idan za ku iya tunawa an wallafa cewa za a bude shafin N-Power a ranar 26 ga watan Yuni, 2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *