Kotu Ta Raba Aure Saboda Rashin Gamsar Da Miji Da Mata Ba Ta Yi

Wata Kotu da ke Unguwar Igando a jihar Legas ta warware auren wata mata da mijinta saboda yace matarsa bata isarsa a duk lokacin da ya kwanta da ita.

Matar mai suna Adenike ta bayyana a kotun cewa kulun Tosin na yi mata gorin cewa bata isarsa kamar yadda sauran matan sa na waje.

“Na auri Tosin shekaru bakwai da suka wuce kuma mun haifi ‘ya’ya biyu amma hakan ba shine ke hana Tosin lakada mun a duk lokacin da ya ga dama. Sannan kuma ga shi da masifar neman mata a waje. A haka kuma sai ya rika zargina da neman maza a waje nima.

Adenike ta roki kotu ta raba aurensu ganin cewa yanzu babu sauran kauna a tsakaninsu.

Shi kuwa mijin nata wato Tosin ya amince da a raba auren duk da yana matukar son matarsa kamar yadda ya shaidawa kotun.

Ya ce tabas yana lakada wa matarsa Adenike duka amma ya yi haka ne saboda ya gano cewa Adenike na bin maza a waje.

A karshe alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya raba auren sannan ya yanke hukunci kula da ‘ya’yan su biyu da wadannan ma’aurata suka haifa wa Adenike.

Sannan ya ce Tosin zai dauki nauyin makaranta da ciyar da ‘ya’yan su biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *