Kaduna: An Kama Angon Da Kashe Amaryarsa Ya Jefa Gawarta A Rijiya

Wani magidanci mai shekara arba’in, Abdulrahaman Abdulkarim ya shiga hannun ‘yan sanda a jihar Katsina saboda zarginsa da ake yi da kashe matarsa da jefa gawarta a cikin rijiya.

Ana zargin Abdulkarim ya aikata laifin ne a kauyen Madabu -Dabawa da ke karamar hukumar Dutsinma na jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis.

Ya ce wadda aka kashe, Wasila Sara, mai shekara 19, amaryar Abdulkarim ce.
“A ranar 14/06/2020 misalin karfe 2 na rana mun samu rahoto cewa wani Abdulrahaman Abdulkarim mai shekara 40 a kauyen Madabu, Dabawa, karamar hukumar Dutsinma na jihar Katsina ya kashe amaryarsa wata Wasila Sada mai shekaru 19 kuma ya jefa gawarta a rijiya.

“Daga nan, DPO na Dutsinma ya jagoranci jami’an zuwa inda abin ya faru, sun gano gawar sun kuma kai ta babban asibiti inda aka tabbatar ta mutu bayan gwaje gwaje da likita ya yi.

“An kama wanda ake zargi da aikata laifin kuma yana taimakawa ‘yan sanda wurin bincike. A halin yanzu ana cigaba da gudanar da bincike.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *