Amarya Ta Kashe Dan Kishiyarta Dan Shekara 8 Ta Hanyar Saka Masa Guba A Dandume, Jihar Katsina


‘Yan Sanda a jahar Katsina sun cafke Wata Matan aure yar shekaru 20, Murja Ibrahim, a kan zargin kashe Dan kishiyanta ta hanyar saka masa guba a cikin abinci.

a wani sanarwa da Kakakin rundunar ya fitar, Gambo Isah, ya ce abun ya faru ne a 19 ga watan Yuni inda wani magidanci IBrahim Sani daga kauyen Dandume ya kawo rahoton matarsa ta biyu, Murja, a ofishin ‘yan sanda dake yankin A kan zargin ta kashe dansa Dan Shekaru 8.

Isah ya ce an aika jami’an yan sanda zuwa inda abun ya faru sanann suka dauki gawar yaron zuwa babbar asibiti dake Funtua inda likitoci suka tabbatar da rasuwar yaron

Kakakin ya ce an cafke wacce ake zargi da aikata laifin sannan kuma tana taimakawa yan sanda wajen gudanar da bincikensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *