‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda 1 Tare Da Wasu Mutane 8 A Katsina

… ‘yan sanda sun ce mutane shida suka kashe har da jami’in su guda daya

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A daren jiya Laraba ne, ‘yan bindiga bisa babura sama da dari suka kai tagawayen hare-hare a kauyukan Kanawa da Kuma Kauyen Kanga da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka kashe mutane takwas da jami’in tsaro daya har lahira, sun kuma jikkata wasu da dama tare da kwashe masu dukiyoyi.

Wani mazaunin garin ya tabbatar wa RARIYA ta waya cewa “yan bindigar sun zo garuruwan ne da misalin karfe biyu na daren jiya, sun ajiye mashinan su wajen gari, inda suka Yi ta harbe-harben har suka kashe mana mutum Takwas, kuma sun jikkata mutane da dama, wanda yanzu haka suna kwance a babbar asibitin garin Danmusa.

Shima Mai magana da yawun rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da kai hare-hare a kauyukan. Inda ya ce Mutum shidda aka kashe a harin na jiya.

Gambo Isa ya kara da cewa a lokacin da muke kokarin kai masu dauki, ashe barayin sun yi mana kwantan bauna, har jami’in mu guda ya rasa ransa. Kuma yanzu haka kwamishinan yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba ya bada umurnin tura karin jami’an tsaro na kwantar da tarzoma. Kuma an tura har da Mukkaddashin kwamishinan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *