Ya Salam! Mahaifi Ya Yiwa ‘Yar Cikinsa ‘Yar Shekara 3 Fyade Yayin Da Matarsa Ke Nakuda A Asibiti (Hotuna)


Wani maigidanci dan Shekaru 43 ya shiga hannu a yayin da ake zarginsa da yiwa yarsa yar shekaru 3 a lokacin da matarsa ke nakuda a asibiti.

Mr. Ikechukwu Ekenta ya kasance dan Ikeduru-Ogwah wanda ke karkashin karamar hukumar Mbaitolu a jahar Imo ana zarginsa da lalata budurcin yar, Kamsiyochukwu Ekenta a ranar 28 ga watan Afrilu 2020 a yayin da matarsa ke nakuda za ta haifan masu da.

A yayin da yarinyar Kamsimyochukwu yar shekaru 3 da Wata 10 take bayyana yadda abun ya faru ta ce babanta ya saka “komkom” (azzakarinsa) a cikin na ta a yayin da take bacci. Ta ce zafin ya tada ta.


A yayin da ya ke magana a cibiyar Professor Dora Akunyili Women Development Center a garin Awka, wanda ake zargi Ikechukwu Ekenta Ya ce Shaidanai suka aikata wannan mummunar aiki.

Ya ce a duk lokacin da shaidanun ya suka shige shi sai ya kama yin abubuwa ba a cikin hayyacinsa ba. Ya ce a ranar ya yi amfani da yatsarsa wajen lalata budurcin Yar na sa a lokacin da shaidanun suka shige shi.

Matar wanda Yayi fyade, Mrs Uzoamaka Ekenta, a yayin da ta ji labarin ta ce daga dawowarta daga asibiti ta gano cewa yarinyar cikin rauni a yayin da take ma ta wanka. Sai ta tambaye yar na ta ta fadawa ma ta cewa mahaifinta ya yi lalata da ita.

Mrs Ekenta ta ce sai ta tambaye mijinta na abunda ya faru sannan ya furta cewa ya aikata abunda ake zarginsa da shi amma ya ce yatsar ya saka ma ta a farginta . Suka garzaya da yarinyar zuwa asibiti inda aka gano cewa Yayi amfani da azzakarinsa wajen yi ma ta fyade ba yatsar kawai ya saka ma ta ba kamar yadda ya fada.

Sai ta fadawa iyayen maigidan na ta amma suka yi barazanar walakanta ta idan ta fadawa wani abunda ya faru

Kwamishinan harkokin da suka shafi mata da yara na jahar Imo, Lady Ndidi Mezue, Ta razana Da jin labarin abunda ya faru. Inda ta yi Allah wadai da abun da mahaifin yayi sannan ta kara da cewa har yanzu yarinyar tana cikin wani hali sakamakon raunin da mahaifinta ya janyo ma ta.

Lady Ndidi ta ce samun labarin ne daga bakin wani Dan TONON asiri, inda ya ce da samun labarin hakan ta sanya jami’an tsaro zuwa gidan wanda ake zargi a Onitsha domin kama shi. Ya ce da yardan Allah sai an masu hukunci wanda ya daidai da laifin da ya aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *