Siyasar Bola Tunibu tazo karshe tunda akai masa gunduwa-gunduwa – cewar Fani kayode.

Mista Femi fani kayode yayi kira ga babban jigo a jam iyar APC Ahmad Bola Tunibu da yayi ritaya daga siyasa kuma ya janye goyon bayansa ga shugaban kasa muhammadu Buhari.

Kayode yayi wannan magana ne bayan shugaban kasar ya bayyana victor Giadom a matsayin mukaddashin shugaban APC adaidai lokacin da kotu ta kori tsohon shugaban APC Adam Oshiomole.

Ga Fani kayode yace:

Da farko akayi fatali da Adam oshiomole ta kotun daukaka kara, se kuma Wanda akaso ya maye gurbin Sa a jam iya Abiola Ajimobi ya fada gargara.

Fani kayode yakara dacewa:

Se kuma aka zakulo babban Dan adawarsa victor Giadom wanda Buhari ya yarda dashi a matsayin shugaban jam iyar APC Na kasa Na riko

Abin nufi. Ta karewa Ahmad Bola Tunibu, anyi jifa dashi Daga cikin motar jam iyar APC, kuma anyi masa ritaya daga siyasa.

Ana tunanin cewa tsohon gwamnan Lagos yana cikin manyan da suka tsayawa Adam oshiomole, kuma Dan siyasar yana harin takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ne.

Masu hasashen siyasa sunce wadanda suke Adawa da Ahmad Bola Tunibu sukai kokarin yin waje da Adam oshiomole, wanda yin hakan Na iya kawowa Ahmad Bola Tunibu cikas a yunkurin Sa Na samun takara.

Sauran bayani Na nan tafe.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *