Hon. Abdullahi Ya Yi Jimamin Rasuwa Tsohon Gwamnan Jahar Oyo Ajimobi

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilai ta kasa ya yiwa iyalai, abokan arziki, da gwamnati jihar Oyo da al’ummar jihar ta’aziyya a kan rasuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Abiola Ajimobi .

Tsohon gwamna, Abiola Ajimobi

Hon. Abdullahi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a yayin da Dan majalisar ya yiwa ‘yan uwan da abokan arzikin mamacin ta’aziyya.

Mamacin ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar korona bairus sannan ya kasance Tsohon gwamnan jahar Oyo. Allah ya jikansa da rahama #amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *