Covid-19: An Killace Shugaban Kasan Senegal

An killace Shugaba kasan Senegal, Macky Sall
Mall ya kasance ya gana da Wani wanda yake dauke da cutar coronavirus.
Duk da cewa dai Sall bai dauke da cutar bayan an masa gwaji amma likitoci sun umurce shi da ya killace kansa na tsawon kwanaki 15.
Fadar Shugaban kasan ta bayyana hakan a wani sanarwa Da ta fitar a ranar Laraba da daddare
A farko dai, ‘Yar majalisar kasar, Yeya Diallo, ta furta cewa ta kamu da cutar.
Diallo ta umurci mutane da su kasance cikin tsabta