Buhari Ya Yi Takaicin Matakin Kasasshen Renon Faransa Na Janyewa Daga Shirin ECO

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jindadi da matakin kasashen renon Faransa na janyewa daga shirin samar da kudin bai daya tsakanin kasashen yammacin Afrika, wanda aka yiwa lakabi da ECO, yayinda ya gargadi takwarorinsa kasashen da ke cikin tattaunawar kaddamar da kudin kan su tashi tsaye wajen cika sharuddan da aka gindaya domin samun nasarar shirin.

Cikin sakon da Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce abin takaici ne yadda kasashen suma suka kirkiri nasu kudin bisa jagorancin Faransar wanda suka sanyawa suna kwatankwacin na kasashen yammacin Afrikan wato ECO.

Shugaban na Nijeriya ya ce za a iya bayyana matakin kasashen renon Faransar da rashin mutunta tattaunawar da kasashen ke tsaka da yi game da batun samar da kudin bai dayan, la’akari da yadda suka dauki wancan mataki na janyewa ba kuma tare da sanar da kowa a hukumance ba.

Ranar 20 ga watan Mayun 2019 ne Faransa ta aminta da janye takardar kudin CFA da take samarwa kasashen mallakinta don hada-hada inda ta bayar da damar samar da sabuwar takardar kudi da ta yiwa suna ECO, kuma kasashen suka aminta duk da cewa akwai waccan tattaunawa tsakaninsu da takwarorinsu na Afrika.

Buhari ya kuma jaddada matsayin Najeriya na aiwatar da kudin, inda ya bukaci kowacce kasa da ta cika sharuddan da aka gindaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *