Bayan Rushe NWC, APC Ta Amince Da Iyamu A Matsayin Ɗan Takarar Gwmana A Edo

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rushe Kwamitin Zartarwa na Ƙasa, NWC na jam’iyyar.

Bashir Ahmad, Hadimin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Kan Sabbin Kafafen Watsa Labarai ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa an ɗauki wannan mataki ne a taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, NEC na Jam’iyyar, wanda aka gudanar ranar Alhamis.

“Biyo bayan shawarar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, an rushe Kwamitin Zartarwa na Ƙasa, NWC na Jam’iyyar APC”, Mista Ahmed ya rubuta haka.

Jam’iyyar ta kuma naɗa Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa kuma Kwamitin Shirya Babban Taron Jam’iyyar na Ƙasa.

A ɗaya ɓangaren kuma, Kwamitin Zartarwar na APC ya amince da Osagie Ize Iyamu a matsayin ɗan takarar gwamna a jihar Edo.

Kwamitin ya ce yadda aka fitar da Mista Iyamu a matsayin ɗan takara akwai adalci a ciki.

Shugaba Ƙasa Muhammadu ya umarci dukkan ‘yan jam’iyyar APC da su janye ƙararrakin da suka shigar a kotuna saboda suna shafar jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *