Zagin Manyan Mutane: An Tsige Albanin Gombe Daga Limanci Juma’a

Kwamitin masu kula da masallacin Jumma’a na miyetti dake jihar Gombe, sun dakatar da shahararran malamin Addinin islama, da ake kira Albanin Gombe.

Kwamitin sun dakatar da malamin daga jan sallar Juma’a kan laifin zagi da aibanta mutane a kan minbari, wanda hakan ya saba dokar kwamitin masallacin.

Idan baku manta sheikh Albanin Gombe yayi kaurin suna wajan yiwa Gwamnatin Nigeria, dama ta jihar Gombe wankin babban bargo kan halin matsin rayuwa da ake ciki, inda yake ta fafutukar ganin gwamnati ta sassautawa al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *