Wasu Tsoffin Masu Gadi 2 Sun Yiwa ‘Yar Shekara 13 Fyaden Gayya A Kumbotso, Jahar Kano


Jami’an hukumar NSCDC reshen jahar Kano ta ce ta kama wasu masu gadi 2 wadanda ake zargi da yiwa yar shekaru 13 fyade a Kumbotso, jahar.
 

Kwamandar hukumar, Abu Abdu, ya tabbatarwa manema labarai da hakan inda ya ce masu fadin sun kasance yan shekaru 56 da 65.

A cewar Abu, wadanda ake zargi sun furta cewa su kan baiwa yarinyar N200 a dukl lokacin da suke so su yi lalata da ita.
 

Abu ya jaddada cewa hukumar tana nan a kan bakanta na ganin cewa ta rage yawan cin zarafin mata da yara a jahar.
 

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da sanya ido a tashoshi, kasuwanni, da ma gidajen da ba a karasa ba inda ake aikata ayyukar da suka karya doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *