Wani Matashi Ya Yiwa Wasu Kananan ‘Yan Gida Daya Fyade

A ranar Talata rundunar ‘yan sanda reshen jahar Ekiti ta gurfanar da wani matashi Dan shekaru 26, Taiwo Odetunde, a kan zargi yiwa wasu mata 2 ‘yan uwan juna wadanda shekarunsu ke tsakanin 13 da 14 fyade bayan ya ja hankalinsu ta hanyar yi masu alkawarin dinka masu Face Mask

Lauyar ‘yan sanda da ta mika karar zuwa kotu, sifeto Monica Ikebuilo, Ta fadawa kotun cewa Oddtunde ya aikata laifin ne a 9 fa watan Yuni, 2002 a Ado-Ekiti.

Ta bukaci kotun da ta bada umurnin Garkame wanda ake zargi har sai lokacin da samu shawarar da take bukata daga ofishin daraktan hukuncin masu laifuka (DPP).

Cif Majistare , Mrs. Adefumike Anoma, Ta ki saurarar neman sassauci da lauyar wanda ke kare wanda ake zargi. Ta bada umurnin Garkame shi a gidan yari har zuwa ranar saurarar karar a 27 fa watan Yuli, 2020z

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *