Nima Ina Cikin Zawara Miliyan 258 Da Ake Da Su A Fadin Duniya – Sadiya Farouq

Ministar Agaji da Ci Gaban Al’umma Sadiya Umar Farouk, ta bayyana cewa a matsayinta na bazawara ta shiga sahun masu murnar zagayowar ranar zawarawa ta duniya wacce ake yinta a duk ranar 23 ga watan Yunin kowacce shekara. 

Sadiya Umar Farouq ta ce kawo yanzu akwai zawarawa a duniya wanda adadin su ya kai kimanin milyan 258.  
Hakazalika Minista Sadiya ta ƙara da cewa zamu cigaba da kare mutuncin kanmu da sauran hakkokin bil-adam na duniya 

Majalisar Dinkin Duniya dai ta keɓe ranar 23 ga watan Yunin kowacce shekara, domin tunawa da halin da matan da suka rasa mazajensu da kuma bukatar tallafa musu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce duk da babu hakikanin alkalumma game da yawan Zawarawa a fadin duniya amma Miliyoyin Zawarawan ne ke cikin mawuyacin hali, sakamakon rasuwar mazajensu, ko kuma tsautsayin rabuwa da Miji.

A wasu kasashen ma zawarawan na fuskantar tsangwama daga jama’a abin da ke jefa rayuwarsu da ta ‘ya’yansu cikin mawuyacin hali.

Akan haka ne Majalisar ta ware 23 ga watan Yuni a matsayin ranar Zawarawa a duniya .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *