Na Zama Abun Firgita Makiyana A Siyasar Jihar Edo – Godwin Obaseki

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kwatanta umurnin da kotu ta bayar na dakatar da shi daga tsayawa takarar zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP a matsayin wani yunkuri ne na magautansa da suke son watsa jam’iyyar.

Obaseki wanda ya bayyana hakan ta bakin mai taimaka masa akan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie, a wata tattaunawa da aka yi da shi ta wayar tarho a ranar Talata, ya yi nuni da cewa, magautan Jam’iyyar PDP sun rigaya sun firgita a kan gagarumin goyon bayan da jam’iyyar ta PDP ke samu daga al’ummar jihar.

Ya ce, “umarnin da kotun ta bayar a daren shekaranjiya. Magautanmu ne da suke a wajen jam’iyyarmu ta PDP suke kokarin kawo rudami a tsakaninmu kamar yanda suka hargitsa Jam’iyyarsu.

“Sun damu a kan gagarumin goyon baya da karbuwar da jam’iyyarmu ta PDP da gwamnatinmu suke samu, hakan ne ya sanya suka firgita wajen neman hanyar hanamu yin takara ta kowanne fanni domin sun san cewa sun riga sun fadi a zaben da za a yi.

Tun da farko dai kwamitin da ke tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC a jihar Edo ne ya haramta wa gwamnan jihar Godwin Obaseki shiga zaɓen fitar da gwani wanda za a gudanar kafin tsayar da ɗantakarar gwamna.

Shugaban kwamitin, Jonathan Ayuba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da rahoton ayyukan kwamitin ga shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole.

Wanda hakn ne ya sanya Godwin Obaseki ya fita daga jam’iyyar APC tare da shiga jam’iyyar PDP. 

Tun da farko Obaseki ya bayyanawa manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja cewa zai koma wata jam’iyyar domin neman takara a wa’adin mulki na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *