An Kama Wanda Ya Yiwa Jaririya ‘Yar Wata 3 Fyade A Nasarawa (Hotuna)


Hukumar NSCDC ta ce jami’anta sun cafke wani matashi wanda ake zargin shi ya yiwa jaririya‘Yar watanni 3 fyade a kauyen Adogi dake jahar Nasarawa.


Hukumar ya bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, inda ya ce jami’an sun cafke matashin ne bayan sun gudanar da bincike a kan lamarin.

”Bayan an gudanar da cikakken bincike a kan lamarin yiwa jaririya yar wata 3 fyade, a Yayind binciken aka kama wani matashin da ake zargin shi ya yiwa jaririya yar wata 3 fyade.” – Inji hukumar NSCDC a shafinta na Twitter.

Idan za ku iya tunawa Mun sakA wannan labarin a makon da ya gabata inda mahaifiyar jaririya, da aka yiwa fyade, Maimuna ta yi bacci da tagar ta bude a dakinta domin ta sha iska Saboda zafi. Sai can an jima a cikin dare ta farka babu jaririyar a kusa da ita. Ai kuwa a nan take, ta fita daga cikin dakin ta neme agajin alumma aka shiga bincikar jaririyar. Daga baya aka ga jaririyar a wani gida wanda ba a karasa ba an cire ma ta kamfenta da jini a fargin ta.

Ita jaririyar a halin yanzu tana asibitin horaswa na Jos (JUTH) inda za a yi ma ta aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *