An Gurfanar Da Maigidan Da Ya Kashe Matarsa Da Jaririnsu A Gaban Kotu

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Osun a ranar Talata 23 ga watan Yuni,2020, ta gurfanar da wani maigidana, Micheal Adenola, a gaban Wata kotun majistare dake gudanar da zamanta a Ile-aide a jahar Osun A kan zargin kashe matarsa, Esther da jariri su Dan wata 14, Glory.

Gangan jikin Esther da jaririnta, Glory, an gano su a wani kwata dake kusa da makarantar firamare na AUD a Isale Agbara, Ike-Ife ba kai a watan Mayu. Binciken yan sanda ya sanya kama Micheal Adunola da Wata mata, Atinuke Olawoyin.

Lauyar da ya mika karar zuwa kotu, Sunday Osamyintuyi, a Yau ya fadawa kotun cewa shi wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Mayu, 2020 da misalin karfe 12:00 na rana a Ile-Ife. Ya yi bayanin cewa shi wanda ake zargi ya hada baki da abokansa wajen kashe matarsa da jaririnsa. Ya ce shi wanda ake zargi ya kashe matarsa da jaririnsa ba isa bisa doka ba sannan ya guntule masu kai.

Osanyintuyi ya ce laifin ya sabuwa sashi 242, da 319(1) da kuma 516 na kundin dokar jahar Osun, 2002.


Majistare Muhibah Olatunji, ta ki saurarar rokan kotun da shi wanda ake zargi yayi. Ya fadawa wanda ya mika karar zuwa kotu da ya kwafin takardar karan ya aika zuwa ofishin daraktan yanke hukunce-hukuncin masu laifuka na jahar domin neman shawarar yadda za a sha kan lamarin.

Olatunji bayan haka ta bada umurnin Garkame wanda ake zargi a gidan yarin Ilesa sannan ta daga Saurarar karar zuwa 28 ga watan Yuni 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *