Shugabancin Najeriya Na Inyamurai Ne A 2023 Duk Wanda Bai Amince Da Haka Ba Bai Son Ci Gaban Kasa – Sanata Jim Nwobodo

Sanata Jim Nwobodo wanda ya kasance gwamnan 2 a a jamhuriyyar Najeriya a tsohuwar Anambra, ya ce Shugabancin kasar nan a hannun inyamurai za ta fada a shekarar 2030.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da manema labarai a gidansa dake Enugu a ranar Litinin 22 fa watan Yuni 2020, Dan siyasar mai Shekaru 80 ya ce shugabancin kasar Najeriya ya kamata ya ta kasance kudancin Najeriya ne domin samar da ci gaba a kasar nan

Ya kara da cewa Duk wanda bai amince da tsayar da inyamuri a Shugabancin kasar nan Bai son ci gaban Najeriya.

”A shekarar 2023 ya kamata ya fito daga kudancin Najeriya. Saboda haka Ina kira ga sauran kasashen da su marawa hakan baya domin ci gaban kasar nan. Ya kamata Kudancin yankin Najeriya ta fitar da Dan takarar Shugaban kasar nan wanda zai gaji Shugabanci daga hannun Muhammadu Buhari.” Ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *