Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Rashin Wani Jarumin Dan Sanda A Delta


Allah ya yiwa mataimakin Shugaban ‘yan sanda na jahar Delta na sashen ayyuka na musamman, DCP Mamman Sale Rijau

Ya rasu ne a daren Litinin da daddare bayan yayi rashin lafiya.

Har yanzu dai ba a san dalilin ya sa ya rasu amma an gano cewa dan sanda yana fama da ciwon suga.

Kwamishinan’yan sanda na jahar Delta, Hafiz Inuwa, ya tabbatarwa manema labarai da rasuwar mataimakin kwamishinan inda ya ce za a ma mamacin janaiza kamar yadda ake yi a addinin musulunci.


“A razane ni ke fadawa al’umma batun rasuwar aboki na, dan uwana sannan kuma abokin aiki na DCP. OPS. DELTA COMMAND –DCP. MAMMAN A. RIJAU a ranar 22/06/2020 a karfe 11:00 na dare.

“Ya rasu ne bayan wani Dan rashin lafiya Da ya kama shi. Za a binne shi kamar yadda Addinin musulunci ta ayyana a birnin Minna, jahar Neja yau Talata 23/06/2020. “Allah ya jikansa da rahamarsa sannan kuma ya yafe masa duk kura-kuransa AMIN” – inji kwamishinan ‘yan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *