Matashin Da Ya Yiwa Alade Fyade Ya Gurfana A Gaban Kotu

A gabata da wani matashi Dan Shekaru 22,Ayokunbi Olaniyi, gaban Wata kotun majistare dake Iyaganku a kan zargin an kama shi Yana jima’i Da alade

Lauyar da ya mika karar zuwa kotu, sifeto Opeyemi Olangunji, ya fadawa kotun cewa Olaniyi Wanda ke zama a unguwar Eleti-Odo a ta hanyar Iwo a Ibadan ya aikata laifin a ranar 2 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00 na yamma 

A cewar Olagunju, ya ce shi wanda ake zargi ya kasance Yana aiki ne a wani gidan gona a Elewi,a ta yankin Odo l, Ibadan. An Kama shi Yana jima’i da daya daga cikin aladun gidan Gonar. An Kama wanda ake zargi ne tare da cajinsa a kotu sakamakon zargin Da ake masa na aika laifin da ya sabawa sashi214 (2) na dokar masu kaifuka Cap 38, Vol. II na dokar jahar Oyo 2000.

Bayan an kama shi, shi wanda ake zargi ya karyata laifin Da ake zarginsa da shi. lauyarsa Mista Mumin Jimoh, ya roki kotun da ta bada belin wanda ake zargi inda ya furta cewa shi mai aladen ya yafe masa.

The presiding magistrate, Olaide Amzat, after listening to his plea, said

”Idan har mai aladen ya yafe masa, Shi Allah ya yafe masa ne Ko ita aladen ta yafe masa? Dole A yi shari’a a kan lamarin.”

Ya bada belin Ayokunbin a kan kudin naira N100,000 Tare Da kawo wakilai 2 wadanda za su tsaya masa 

daga nan ya daga saurarar karar zuwa 21 fa watan Yuli 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *