Kotu Ta Dakatar Da Jam’iyyar PDP Daga Gudanar Da Zaben Fidda Gwanin Gwamnan Jahar Edo

Wata babbar kotu dake zamanta a birnin Fatakwal a jahar Ribas ta dakatar jam’iyyar PDP reshen jahar Edo gudanar da zaben fidda gwamnan jahar wanda za a gudanar a ranar 25 fa watan Yuni, 2020.

Karar wanda aka mikawa kotun a ranar Litinin 22/6/2020 wanda daya daga cikin masu son tsayawa takarar gwamnan jahar a jam’iyyar, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya mika yayin da ya ce shi ba zai janyewa gwamna Godwin Obaseki ba.

Alkalin kotun ya bada umurnin dakatar zaben fidda gwanin sannan kuma a bar wanda ya mika karar ya tsaya a gudanar da zaben da shi. A karshe Alkalin ya daga saurarar karar zuwa 24/6/2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *