Katsina: Mata 32 Sun Haihu A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

Kimanin mata talatin da biyu ne, suka haifu a sansanin ‘yan gudun hijira da ke wata Makarantar firamare ta garin Faskarin Jihar Katsina.

Akalla sama da yan gudun hijira dubu bakwai ne suka baro kauyukan su, sakamakon hare-haren yan bindiga suka kai masu a kauyukan karamar hukumar Faskari.

Majiyarmu ta tabbatar Mata da ce ana samun taimakon kayan abinci daga Gwamnatin Jihar Katsina da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun Jama’a. Kuma duk sadda zaa dora abincin akan dafa shinkafa sama da biyar a lokaci daya.

A wani labarin kuma, Gwamna Aminu Bello Masari ya tallafawa al’ummar garin Kadisau, da ke karamar hukumar Faskari, domin rage masu radadin halin da suka tsinci kansu.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa duk gidan da yan bindigar suka kashe an basu, naira dubu dari daya, su kuma wadanda suka ji raunuka an baiwa kowanne su naira dubu hamsin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *