Duk Matsalar Da Ya Shafi APC Tamkar Ya Shafi Najeriya Ne – Sanata Lawan

Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya bayyana cewa duk matsalar da ya samu jam’iyyar APC tamkar ya samu najeriya ne domin najeriya da APC kamar Danjuma ne da ‘Dan-Jummai.

Sanata Lawal ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Sanata Lawan ya ce baya ga tattauna matsalar tsaro da ya addabi musamman jihohin Arewacin Najeriya, ya tattauna da shugaba Muhammadu Buhari game da matsalolin da ke neman dulmiyar da jam’iyyar APC a Najeriya.

” Mun tattauna mai zurfi da shugaba Buhari game da tabarbarewar tsaro a kasar nan musamman yankin Arewacin Najeriya, na shaida shugaba Buhari halin da ake ciki da kiraye-kirayen da wasu ke yi saboda matsin da suka fada a dalilin rashin tsaro.

” A gaskiya lokaci yayi da dole manyan hafsoshin tsaron Najeriya su maida hankali domin kawo karshen wannan matsala. Idan mutum ba zai iya ba, ya ajiye aikin, shine ya fi dacewa bawai kullum a ce za a gyara amma kuma gyarar ya gagara ba, Kullum jiya iyau.

” Bayan haka Sanata Lawan ya tattauna batun danbarwar da jam’iyyar APC ta fada ciki.

” APC ce ke da shugaban kasa, gwamnoni masu yawa, duka komai na karkashin mulkin jam’iyyar APC a Najeriya, idan ta samu kanta cikin halin kaka nika yi to kowa sai ya ji a jikin sa a Najeriya. Dole a dinke barakar da ta dabaibaye jam’iyyar tunda wure. Hakan duk na daga cikin abubuwan da muka tattauna da shugaba Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *