Dan Wasan Tennis Na Daya A Duniya ‘Novak Djokovic’ Ya Kamu Da Korona

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan Tennis na daya a Duniya Novak Djokovic ya kamu da cutar korona, wanda ya zama dan wasa na hudu da ya kamu da cutar bayan buga wasa a Adria tour da ya shirya a Croatia.

Batun cewa cutar hadin baki ce ga Djokovic ba bakon abu ba ne.

Ya kuma bayyana cewa shi yana adawa da rigakafin cutar yayin wata tattaunawar kai tsaye da aka yi da shi a shafin Facebook a watan Afirilu.

Ya ce ” babu wanda ya isa ya tursasa ni a yi mani riga kafi” shin hakan zai iya zama dole ga matafiyi da kuma wanda zai buga gasar.

Kuma an ta samun masu goya masa baya kan kin amincewa da allurar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *