Watan Shawwal Ya Cika Kwana 30 A Najeriya- Sarkin Musulmi

Kwamitin Bada Shawara Kan Harkokin Addini na Fadar Sarkin Musulmin Najeriya, bisa haɗin gwiwar Kwamitin Duban Wata na Ƙasa bai samu ko rahoto ɗaya ba daga kwamitocin duban wata daban-daban a faɗin ƙasar nan dake tabbatar da ganin jinjirin watan Zulƙi’ida, 1441 ranar Lahadi, 21 ga Yuni, 2020 daidai da 29 ga Shawwal, 1441.

Kwamitin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa wadda Shugaban Kwamitin, Farfesa Wali Junaidu ya sanya wa hannu.

Kwamitin ya ce saboda haka, yau Litinin ita ce 30 ga Shawwal, 1441, daidai da 22 ga Yuni, 2020.

A cewar Kwamitin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad, III ya karɓi rahoton, ya kuma bayyana Talata, 23 ga Yuni, a matsayin 1 ga Zulki’ida, 1441 a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *