Rashawa: An Bukaci EFCC ta binciki Mustapha Inuwa Kan Batar Biliyan N1.6

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a shekara ta 2015 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NPC Abdulmumini Shehu Sani ya bukaci hukumar yaki da cin-hanci da yiwa tattalin arziki fasa-kauri EFCC  da ta sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa kan batan wasu kudade kimanin Naira Biliyan 1.6.


Wannan na ɗauke ne cikin wata takarda da shugaban jam’iyyar na NPC ya aikewa da shugaban hukumar ta EFCC a ranar 17 ga Mayu 2017.

Sani ya bayyana cewa babu ta yadda za a yi ace an kashe wadannan makudan kudade kamar yadda sakataren gwamnatin ya bayyana a lokacin, domin babu wasu makamai da aka saya, kuma jami’an tsaron da aka kawo domin dakile ayyukan ta’addanci basu isa su lashe wannan kudade, kuma a cewarsa jihar tasu ta Katsina bata fama da ayyukan ‘yan Boko Haram.

Sannan daga karshe ya ja hankalin hukumar ta EFCC akan ta gudanar da bincike domin zakulo gaskiya lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *