Ko Ku Kawo Karshen Ta’addanci Ko Kuma Ku San Inda Dare Ya Ma Ku – Inji Lawan

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya kayyade wa manyan hafsoshin tsaron kasar nan wa’adin magance matsalar tsaro ko kuma ya kore su idan suka kasa.

Ahmed Lawan ya ce rayukan ‘yan Najeriya sun fi komai muhimmanci kuma kare su shi ne babban aikin gwamnati don haka dole ne hafsoshin tsaron su yi aikinsu yadda ya kamata ko su san na yi, tun da sun gaza.

“Ba zai yiwu a yi ta tafiya haka ba, dole a kayyade lokacin magance matsalar. Yanzu matsalar tsaro musamman ta Boko Haram da ‘yan bindiga a yankin Arewa, ita ce abu mafi kamata a magance.

Ya ci gaba da cewa,  “Dole su tashi su yi aikinsu ko kuma a kore su”, domin gwamnati ba ta da zabi face ta magance matsalar, sannan wajibi ne a wadata hukumomin tsaro da kayan aiki da ma’aikata domin su yi aikinsu yadda ya kamata.

Ahmed Lawan ya bayyana hakan ne bayan yi wata ganawa da Shugaba Buhari a ranar Asabar, inda ya ce sun tattauna ne kan matsalar tsaro da ke addabar yankin arewancin ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *