Covid-19: Za Mu Garkame Duk Malamin Da Ya Bude Makarantar Islamiyya – Ganduje

Kwamishinan ilimi Na jahar Kano Sunusi Maji Dadin Kiru yace zasu hukunta duk wani malami da aka kama ya karya doka wajen bude makarantun islamiyya A jahar Kano.

Ya kara da cewa bude makarantun islamiyoyi A wanan lokacin zai jefa rayuwar dalibai cikin hatsari inda ya gargadi malaman makarantun islamiyoyi da kada wanda ya kuskura ya bude makaranta har sai humumar ilimi ta jahar Kano ta bada umarnin haka

“Duk wanda muka Kama ya karya Mana doka zamu dauki tsatstsauran hukunci”.

Kwamishinan Yana wanan jawabine Kai tsaye A tashar rediyo ta vision dake Kano yayi da yake amsa tambayoyi Akan batun komawa makaranta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *