Covid-19: An Soke Gasar Firimiyar Najeriya

An soke gasar ajin Firimiyar Najeriya ayammacin jiya Lahadi bayan da shuwagabannin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan guda 20 sukayi wani zama na musamman na yadda za ayi a kammala gasar wato kakar wasa ta 2019 zuwa 2020.

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 17 sun zaɓi a soke gasar gabadaya amma akwai sharaɗin cewar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda uku na saman teburin gasar ta bana sune zasu wakilci ƙasar nan a gasoshin nahiyar Afrika guda biyu wato gasar zakarun nahiyar Afrika da kuma gasar ajin ƙwararru.

Yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rangers ta bayyana cewar itafa saidai ayi wasannin Super Six wato wasannin ‘yan shida kamar yadda akayi a kakar wasan data gabata inda ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Akwa United da kuma Lobi Stars sukabi sahunta.

Haka dai a zaman da akay na yammacin jiya Lahadin an bayyana cewar babu ƙungiyar ƙwallon ƙafan data sami koma baya wato komawa aji na biyu na gasar ta Ajin Firimiyar ƙasar nan, kamar yadda ƙungiyoyin guda 20 suka fafata gasar to sun zasu dawo suci gaba a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *