Covid-19: An Kafa Kwamitin Sake Buɗe Makarantu A Kano

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya kafa kwamitin da zai yi bita kan batun sake bude makarantun da aka rufe tun da farko, don dakile yaduwar cutar cobid-19.

Kwamishinan ya bukaci membobin kwamitin da su hanzarta daukar mataki akan lokaci tare da hanyoyin da za su saukaka yadda za a bude makarantun.

Kwamitin wanda yake karkashin jagorancin Daraktan gudanarwa da ayyukan na ma’aikatar ilimi, Comrade Dalha Isah Fagge yana daga cikin abubuwan da za su gabatar bada shawarwarin da za a yi amfani da su wajen sauƙaƙe sake buɗe makarantu musamman batun samar da tazara tsakanin dalibai.

Membobin kwamitin sun hada da Shugaban Zartarwa na (SUBEB), Sakataren zartarwa na makarantun sakandire ta Kano da kuma Sakataren hedikwatar makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *