Ban Yi Murabus Daga Kujera Na Ba, Sauya Sheka Na Yi Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP – Inji Mataimakin Gwamnan Jahar Ondo

Biyo bayan yin murabus nasa daga jam’iyyar APC, mataimakin gwamnan jahar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi watsi da maganar cewa zai yi murabus daga kujeransa a matsayin mataimakin gwamnan jahar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.

A cewar Agboola, wanda a ranar Lahadi ya yi rajistar zama mambar jam’iyyar PDP ya ce al’ummar jahar suka zabe shi Saboda haka zai ci gaba da yi masu aikin da suka zabe shi Yayi.

Rahotanni a ranar Lahadi sun bayyana yadda mataimakin gwamnan jahar ya sauya sheka daga jam’iyyar APC ya bar gwamnansa a jam’iyyar wanda aka Zabe su a shekarar 2016.

Da yake tattaunawa da yan jarida bayan ya yanki katin zama mamban jam’iyyar PDP, Agboola, ya ce ya yi murabus me daga jam’iyyar APC ne ba wai daga kujeransa ba a matsayin mataimakin gwamnan jahar.

“Al’ummar jahar ne suka zabe ne. Ba su bukaci na yi murabus ba, Saboda haka zan kasance mataimakin gwamnan jahar. An zabe ni ne a matsayin mataimakin gwamnan jahar.” Agboola ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *