‘Yan Sanda Sun Kama Wasu ‘Yan Karota Da Suka Karya Wani Magidanci A Kano (Hotuna)

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu jami’an KAROTA da ake zargin su da lakadawa magidanci duka wanda ya yi sanadin kakkaryewarsa.

Zuwa yanzu kwamishinan ‘yan sandan Kano CP Habu Sani ya yi umarnin mayar da binciken zuwa shalkwatar ‘yan sanda dake Bompai.

Wata majiyar ‘yan sanda ta ce kame jami’an Karotar ya fusata hukumar wacce ta kai ga janye jami’an ta daga titi, koda yake mai magana da yawun KAROTA, yace ba wannan dalili ne ya sa jami’an janyewa daga titi ba.

Kuma ya ce babu tabbacin cewar ‘yan karota ne suka aikata wannan mummunan aiki. Amma bincike zai bayyana gaskiya.

Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya tabbatar da faruwar wannan kwabewar aiki amma ya ce ana cigaba da bincike.

Kwana biyu dai Ana samun tangarda a yanayin tafiyar da aikin Karota a Kano, domin ko a makon jiya wani dan Karota ya jikkata wani matashi sakamakon jona masa wata na’ura mai kashe jiki.

Da yawan mutane na kalubalantar hukumar ta Karota bisa yadda take wuce makadi da rawa wajen ayyukan ta, inda masana shari’a ke cewar hatta cin tarar kudi da karota keyi a yanzu ya saba da doka, domin kotu ce kadai ke da ikon cin tarar mutane idan an tabbatar da laifin su kuma kotuna suna hutun Korona amma kuma a hakan jami’an na cigaba da cin tarar mutane.

Haka ma maganar dokar hana goyon babur da KAROTA ta ayyana Shima masana sharia na cewar wannan tamkar shiga sharo ne ba shanu.

Okey Me ye ra’ayina ku bisa ayyukan jami’an Karota? Aikin na kyau su cigaba da gashi, ko kuwa akwai kura kurai dake bukatar gyara?

Daga Nasiru Salisu Zango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *