‘Yan Bindiga Sun Ƙara Hallaka Mutane Dama A Kauyuka A Katsina

Harin da ‘yan bindiga suka kai, da yammacin Juma’a a garuruwan Kasai da kuma Nahuta a Karamar Hukumar Batsari ya yi sanadiyyar rasuwa yara tara, sakamakon kaduwa da hirgita da kuma gudun ceton rai da matan garin Nahuta suka yi, suka bi ta wani gulbi inda kananan yaran guda tara ciki har da jariri da ya sulbe daga bayan Mahaifiyarsa.

Hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ya tabbatar RARIYA ta waya cewa barayin ne suka zo suka zagaye garin Kasai, amma labarin da muke samu barayin su ukku ne, wajen wani Alhaji Inusa Rigabza ne, akwai sabani tsakanin su kuma nan take suka kashe shi. Karar habin bindigar da suka ji a Kasai da Nahuta suka bar gidajen su da Yara ga kuma ruwan jiya, da muka samu, wasu ratse saboda hirgita, sai ka biyo ta wajen wani Dam, yayansu kanana ruwa ya tafi da wasu har su Tara, an tsamo gawar shidda ukku ake nema, zuwa gobe Sarkin Ruwa ya ce zaa samu gawarwakin su saman ruwa.

Sarkin Ruma ya ce a jiya wadannan yan bindiga sun yi sanadiyyar kashe mutum goma a Karamar Hukumar Batsari, sun kashe daya, tara kuma sun fada ruwa sakamakon firgita. Kuma shekarunsa irin shidda zuwa bakwai, har da jariri guda na goye, yana bayan Mahaifiyarsa ya kucce.

Ga shi sun hana mu noma, ko ka yi shuka za su turo shanun nasu su cinye kuma baa Kama su, mun rasa yadda za mu da su, abun duk ya dame mu. Ranar litinin din nan mai zuwa da azumi za mu tashi da niyyar Allah ya kawo mana karshen wannan tashin hankali a karamar hukumar Batsari da jihar Katsina baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *