Yadda Kawu Na Dan Boko Haram Ya Min Fyade, Ba Zan Tabawa Yafewa Mayakan Ba – Inji Wata Yarinya

Wata yarinya wacce kawunta ya kasance daya daga cikin mambobin Mayakan Boko Haram ta bada labarin yadda kawun na ta ya ma ta fyade sannan abun ya canza ma ta yanayin rayuwarta.

Yarinyar ta ce abun ya faru ne a lokacin da mayakan suka kaiwa kauyensu hari inda suka kashe mazajen kauyen sannan kuma wasu mata suka shiga gudun hijira. Ta bayyana cewa an kashe kawunta ne sakamakon wani Rikici Da ya barke tsakanin kawun na ta da wani mambobin Boko Haram inda bayan hakan ne ya sa aka daura ma ta aure da wani mamban kungiyar daban.


A yayin da take magana da manema labarai a ranar 19 ga watan Yuni, ( ranar da majalisar Dinkin Duniya ta killace domin magana a kan fyade da lalata da mata da ake yi a fadin Duniya), yarinyar ta ce;


“Abun ya faru ne a ranar Talata bayan Mayakan Boko Haram sun shiga kauyen mu, inda suka kashe mazan kauyen Tare Da Kona gidajen sannan suka sace mu mu matan da bamu samu damar tserewa ba suka tafi damu.

”Kawu na, wanda ya kasance mamban mayakan Boko Haram ne ya fadawa ma ni na tashi na bi shi, a nan take ya ce na zama kayan mallakarsa. Tun daga ranar ya dinga min fyade.

“An kashe shi ne bayan ya samu wani matsala tsakaninsa da wasu mambobin Boko Haram. Bayan rasuwarsa aka aura ma ni wani mamban Mayakan.”


Yarinya tana makarantar sakandare sannan tana sa ran Wata rana za ta zama soja, ta bayyana irin dadin Da Ta ji tare da sauran mata a lokacin da suka isa sansanin ‘yan gudun hijira dake Bama.

Ta kara da cewa;


“Duk inda mu ka je, mutane na kiran da sunan matar ‘yan boko haram kamar laifin mu me. Ni ba zan taba yafewa mambobin Boko Haram ba har Duniya ta nade sakamakon abunda suka ma ni.

“Ni a rayuwa na na so na kammala makaranta na na zama soja, sai na tuka jirgin sama na ta kashe Mayakan Boko Haram da bama-bamai. Ina so na ya karshen su (Mayakan Boko Haram) a Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *