Na Sace Kamfen Kwastoma Na Ne Domin Na Yi Asiri Kudi Da Shi – Inji Wani Mai Gyaran Taya


Wani mai gayaran taya Motar , Dele Ope, wanda ya shiga hannun ‘yan sanda a kan zargin Satan kamfen Wata kwastomarsa.


Ope ya ce ya Saci kamfen ne domin ya je Yayi asirin samun kudi Da shi sannan Yana shirin kaiwa bokarsa wanda zai taimaka masa wajen yin asirin

Jami’in hulda Da jama’a na rundunar yan sanda, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar hakan a ranar Lahadi.

Oyeyemi ya ce dan Shekaru 22 mai gyaran tayar an kama shine bayan Wata mata ta kai kararsa zuwa ofishin ‘yan sanda dake yankinsu bayan ya fahimci cewa kamfenta ya bata a yayin da mai gyaran ya bar gidan na ta.

Matar wacce ba a bayyana sunanta ba ta ce ta gayyaci mai gyaran tayan gidanta ne domin ya taya ta gyaran tayar motar ta.

Amma bayan shi wanda ake zargi ya bar gidanta sai ta gano cewa kamfen Da Ta shanya a bisa kan igiyar shanya ya bata.

An take aka shiga neman shi wannan mai gyaran tayar tunda shi kadai ne ya shiga gidan a wannan lokacin.

Shugaban ofishin ‘yan sanda na wannan yankin Warewa, SP Folake Afeniforo, ta aika jami’anta dake karkashinta zuwa Nemo shi matashin tare da kama shi.

‘Yan Sanda sun bayyana cewa suna kama shi suka shiga binciken gidansa a nan ne aka tsinci kamfen matar.


A yayin da ake yiwa wanda ake zargi tambayoyi, Ope ya furta laifin Da ake zarginsa da shi sanna ln ya bayyana cewa zai kai kamfen ne wajen bokansa domin a yi masa asiri kudi.,” Oyeyemi ya ce.


Kwamishinan ‘yan sanda na jahar Ogun, CP Kenneth Ebrimson, ya bada umurnin cajin wanda ake zargi zuwa kotu Da zaran an gama gudanar da bincike a kan lamarin.Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *