Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Hana Mataimakin Gwamnan Ondo Fita Daga Gidan Gwamnatin Jihar Don Ya Sauya Sheka Daga APC (Bidiyo)


Rikici ya barke a gidan gwamnatin jahar Ondo jiya a yayin da kwamishinan ‘yan sanda, Salami Amidu Bolaji, na jahar ya hana mataimakin gwamnan jahar fita daga gidan gwamnatin jahar dake Akure.


Wannan bidiyon ya nuna lokacin da kwamishinan ‘yan sandan Ke cece ku ce Tare Da mataimakin gwamnan, Mista Ajayi. Dalilin yin hakan shine an samu labarin cewa mataimakin gwamnan zai sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP wanda za ku je kwamishinan ‘yan sandan na nanatawa a bidiyo amma a harshen turanci.


Rahotanni daga kafafen yada labarai na Sahara Reporters sun ruwaito cewa zai sauya sheka ne daga jam’iyyar APC zuwa PDP Saboda ya fito takarar gwamna domin ya samu karawa da gwamnan jahar, Akeredolu, a zaben Gwmanan jahar wanDa za A gudanar a 10 fa watan Oktoba 2020. Hakan ya janyo masu ruwa da tsaki suka roki Ajayi a kan kada yayi hakan amma ya ki.


Wani majiyar mu ya bayyana mana cewa mataimakin gwamnan ya yanke hukunci tsayawa takara ne sakamakon rikicin dake tsakaninsa Da gwamnan, Rotimi Akeredolu, bayan zaben 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *