Kungiyar CAN Ta Dakatar Da Sakatarenta Kan Lashe Kudaden Kungiyar

Kungiyar Kiristoci reshen jahar Adamawa ta dakatar da sakataren ta, Mr. Anthony Elishama, a kan zargin albazaranci da kudi naira miliyan N1,350,00.


An dakatar da sakataren ne na tsawon watanni 3, inda aka ba shi tsawon wannan lokaci ya dawo da kudin da ya lashe.

Dakatarwar ya zo kunshe ne a wani sanarwa da Shugaban kungiyar CAN na reshen jahar, Bishop Stephen Mamza, ya fitar yayin da ya umurci Anthony Elishama da ya mayar da kayayyakin Mallakar kungiyar ga sakatariyal kungiyar dake birnin Yola ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwa wanda aka fitar a ranar Asabar da yamma, Mamza ya bayyana cewa dakatar da Elishama ya biyo bayan zaman da majalisar kungiyar ta yi a ranar Alhamis.

A cewar Shugaban kungiyar, “Am dakatar da Mr. Anthony Elishama sakamakon albazaranci da kudin kungiyar naira miliyan N1.350 wanda ya kasance na NIREC.”


Ya ce majalisar zartawar na kungiyar ta nuna rashin jin dadinta game da abunda sakataren yayi inda ya kara da cewa kungiyar CAN ba ta wasa da abunda ya shafi harkar kudi.

Ya dakatar da sakataren zai fara ne a ranar 20 ga watan Yuni, 2020 har zuwa ranar da kwamitin bincike a kan lamarin ta yanke Hukuncin karshe a kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *