Ku Rinka Zaben Mutane Masu Nagarta- Inji Sakataren Jam’iyyar APC


Mataimakin Sakataren jam’iyar APC na jihar Jigawa, Alhaji Sani Magaji Kangire, ya yi kira ga masu zabe da su rinka zaben mutane masu nagarta kula da bukatu da kuma burinsu a ko da yaushe.


Ya yi wannan kiran ne a lokacin kaddamar da rabon kekunan dinki da injinan markade da kayan sana’ar aski da babura da kuma takin zamani da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birnin kudu/Buji Engineer Magaji Da’u Aliyu ya samar ga ‘yan mazabarsa.


Alhaji Sani Magaji Kangire wanda ya bayyana dogaro da kai a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin kowacce al’umma, ya ya hankalin wadanda suka amfana da su guji sayar da kayayyakin.


A jawabinsa na maraba, Alhaji Tijjani Yayari, ya yabawa dan majalisar bisa jajircewarsa wajen kawo abubuwan jin dadin jama’a inda ya bayyana bukatar wanzuwar hadin kai da fahimtar juna a cikin jam’iyar APC.


A nasa jawabin, shugaban jam’iyar APC na KH Buji Alhaji Nuhu Umar, yace jam’iyar tana lura da kokarin kowanne zababbe inda ya yabawa dan majalisar tarayyar saboda kokarinsa na bunkasa tattalin arzikin jama’ar da yake wakilta.


A sakon sa ga taron, Engineer Magaji Da’u Aliyu wanda mai taimaka masa Barrister Murtala Isah Abubakar, yace manufarsa a siyasance za ta ci gaba da mayar da hankali ga kawo sauyi a rayuwar jama’a ta kowacce fuska.


Wasu da suka amfana da tallafin Malam Magaji Gidan Rafa Buji da Nazifa Musa Birnin kudu sun godewa dan majalisar tarayyar bisa wannan karimci tare da alwashin amfani da tallafin ta hanyar da ta dace domin dogaro da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *