Gwamnati Ta Kona Gidan Masu Sace Mutane A Calabar

Gwamnatin jahar Ribas ta bada umurnin kona wani gida kurmus wanda ake zArgin gidan masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Calabar ta kudu a jahar Ribas.

Wani wanda ake zargin mai satan mutane, Edet Effiong Nyong ya kasance cikin wadanda ake zargin masu satan mutane ne sannan Gwamnatin jahar na nemansu ruwa a jallo

A kudancin Rahotanni sun bayyana cewa tawagar da aka sanya bankawa gidan wuta sun hada da mai baiwa Gwamnatin jahar shawara a kan harkokin Da suka shafi tsaro na kudu, Mr Ani Esin, Tare Da DSS Da kuma masu ruwa da tsaki na jahar.


Gidan wanda ke layin Esiere Ebom karamar hukumar Kudancin Calabar a kona shi ne a ranar Asabar.

An samu labarin shi wanda ya mallaki gidan Yana daya daga cikin wadanda ake zargi da sace mahaifin tsohon daraktan hukumar tsaro na farin kaya wato DSS sannan kuma Da shi aka kitsa Shirin sace wani Dan uwan mataimakin gwamnan Jahar, Barr. Efiok Cobham.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *