Da Duminta: Mataimakin Gwamnan Jahar Ondo Ya Yi Murabus, Ya Sauya Sheka Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP


Mataimakin gwamnan jahar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi murabus daga jam’iyyar APC bayan ya kwashe watanni Yana fada da gwamnan jahar, Gwamna Rotimi Akeredolu

Ajayi Yayi murabus daga jam’iyyar APC ne a kauyansa Kiribo, gunduma ta 2, Apoi, wanda ke karamar hukumar Ese-Osi a jahar Ondo a ranar Lahadi 21 fa watan Yuni 2020 awanni kadan bayan kwamishinan ‘yan sanda na jahar, Bolaji Salami, ya hana shi fita daga gidan gwamnatin jahar  


Agboola Ajayi ya karbi katin zama mamban jam’iyyar PDP a nan take bayan Yayi murabus daga jam’iyyar ta APC inda ya ce ya ji dadin komawa jam’iyyar adawar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *